Mark 14

An Shafe Yesu a Betani

1To, Bikin Ƙetarewa da kuma Bikin Burodi Marar Yisti kuwa sun rage kwana biyu a yi, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suna neman wani dalilin kawai su kama Yesu, su kashe. 2Suka ce, “Ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su yi tawaye.”

3Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutum da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tandu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tandun, ta kuma zuba turaren a kansa.

4Waɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, cikin fushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka? 5Da an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi
Girik fiye da dinari ɗari uku
na shekara guda, kuɗin kuma a ba wa matalauta. Sai suka tsauta mata cikin fushi.”

6Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni. 7Matalauta kam suna tare da ku kullum, za ku kuma iya taimakonsu duk lokacin da kuke so. Amma ni ba zan kasance da ku kullum ba. 8Ta yi abin da ta iya yi. Ta zuba turare a jikina kafin lokaci, don shirin janaʼizata. 9Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi waʼazin bishara koʼina a duniya, za a faɗi abin da ta yi, domin tunawa da ita.”

10Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun, ya je wajen manyan firistoci don yǎ bashe Yesu a gare su. 11Suka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafin ba da shi.

Abincin Yamma na Ubangiji

12A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga alʼada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu yi maka shirin cin Bikin Ƙetarewa?”

13Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa, ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi. 14Gidan da ya shiga, ku gaya wa maigidan cewa, ‘Malam yana tambaya: Ina ɗakin baƙina, inda zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina?’ 15Zai nuna muku wani babban ɗakin sama da aka shirya domin baƙi. Ku yi mana shirin a can.”

16Almajiran suka tafi, suka shiga cikin birnin, suka kuwa tarar da kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.

17Da yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun. 18Yayinda suke cin abinci a tebur, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗaya daga cikinku zai bashe ni, wani wanda yake ci tare da ni.”

19Suka cika da baƙin ciki, da ɗaya-ɗaya suka ce masa, “Tabbatace, ba ni ba ne, ko?”

20Ya ce, “Ɗaya daga cikin Sha Biyun ne, wanda yake ci tare da ni a kwano. 21Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda yake a rubuce game da shi, amma kaiton mutumin da ya bashe Ɗan Mutum! Zai fi masa, da ba a haife shi ba.”

22Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, “Ku karɓa, wannan jikina ne.”

23Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki.

24Sai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa. 25Gaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga ʼyaʼyan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ ”

26Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.

Yesu Ya Yi Magana a kan Mūsun Bitrus

27Yesu ya ce musu, “Dukanku za ku ja da baya ku bar ni, gama yana a rubuce, cewa:

“ ‘Zan bugi makiyayin tumaki,
tumakin kuwa za su warwatse.’
Zak 13.7

28Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”

29Bitrus ya ce, “Ko da duka sun ja da baya suka bar ka, ba zan bar ka ba.”

30Yesu ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, yau-I, da daren nan-kafin zakara yǎ yi cara sau biyu
Waɗansu rubuce rubucen hannu na farko farko ba su da sau biyu.
kai da kanka za ka yi mūsun sanina sau uku.”

31Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi, ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka.

Getsemane

32Suka tafi wani wurin da ake kira Getsemane, Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, yayinda ni kuwa in yi adduʼa.” 33Ya tafi tare da Bitrus, Yaƙub da kuma Yohanna. Sai ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai. 34Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har ma kamar zan mutu. Ku dakata a nan ku yi tsaro.”

35Sai ya yi gaba kaɗan, ya fāɗi a ƙasa, ya yi adduʼa, ya ce in mai yiwuwa ne, a ɗauke masa wannan saʼa. 36Ya ce, “Ya Abba,
da Aramayik na Baba
Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so.”

37Sai ya koma wajen almajiransa, ya same su suna barci. Ya ce wa Bitrus, “Siman, kana barci ne? Ka kāsa yin tsaro na saʼa ɗaya? 38Ku yi tsaro, ku kuma yi adduʼa, domin kada ku fāɗi cikin jaraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”

39Ya sāke komawa, ya maimata adduʼar da ya yi. 40Da ya dawo, ya sāke tarar da su suna barci, domin barci ya cika musu ido. Suka rasa abin da za su ce masa.

41Da ya koma sau na uku, sai ya ce musu, “Har yanzu kuna barci, kuna hutawa ba? Ya isa! Lokaci ya yi. Duba an ba da Ɗan Mutum a hannun masu zunubi. 42Ku tashi! Mu tafi! Ga mai bashe ni ɗin yana zuwa!”

An Kama Yesu

43Yana cikin magana ke nan, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun ya bayyana. Ya zo tare da taro da suke riƙe da takuba da sanduna. Manyan firistoci da malaman dokoki, da kuma dattawa ne suka turo taron.

44Mai bashe shi ɗin ya riga ya shirya alama da su, cewa, “Wanda na yi wa sumba, shi ne mutumin, ku kama shi, ku riƙe sosai.” 45Nan da nan Yahuda ya je wurin Yesu, ya ce, “Rabbi!” Ya kuma yi masa sumba. 46Mutanen kuwa suka kama Yesu, suka riƙe shi. 47Sai wani cikin waɗanda suke tsattsaye kusa ya zāre takobinsa, ya sare kunnen bawan babban firist. 48Yesu ya ce, “Ina jagoran wani tawaye ne da kuka fito da takuba da kuma sanduna domin ku kama ni? 49Kowace rana ina tare da ku, ina koyarwa a filin haikali, ba ku kama ni ba. Amma dole a cika Nassi.” 50Sai kowa ya yashe shi ya gudu.

51Wani saurayin da ba ya sanye da kome sai rigar lilin, yana bin Yesu. Da suka yi ƙoƙarin kama shi, 52sai ya gudu ya bar rigarsa, ya gudu tsirara.

A Gaban Majalisa

53Suka kai Yesu wajen babban firist, sai dukan manyan firistoci, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru. 54Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin filin gidan babban firist. A can, ya zauna tare da masu gadi, yana jin ɗumin wuta.

55Manyan firistoci da dukan ʼyan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba. 56Da yawa suka ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidarsu ba ta zo ɗaya ba.

57Sai waɗansu suka miƙe tsaye, suka ba da wannan shaida ƙarya a kansa, suka ce, 58“Mun ji shi ya ce, ‘Zan rushe wannan haikali da mutum ya gina, cikin kwana uku, in sāke gina wani wanda ba ginin mutum ba.’ ” 59Duk da haka ma, shaidarsu ba ta zo ɗaya ba.

60Sai babban firist ya tashi a gabansu, ya tambayi Yesu, ya ce, “Ba za ka amsa ba? Wane shaida ke nan waɗannan mutane suke kawowa a kanka?” 61Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba.

Babban firist ya sāke tambayarsa, ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?”

62Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama.”

63Babban firist ya yage tufafinsa, ya yi ce, “Ina dalilin neman waɗansu shaidu kuma? 64Kun dai ji saɓon. Me kuka gani?”

Duka suka yanke masa hukuncin kisa.
65Sai waɗansu suka fara tattofa masa miyau, suka rufe masa idanu, suka bubbuge shi da hannuwansu, suka ce, “Yi annabci!” Masu gadin kuma suka ɗauke shi, suka yi masa duka.

Bitrus Ya Yi Mūsun Sanin Yesu

66Yayinda Bitrus yake ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya, baiwa, ɗaya daga cikin maʼaikatan babban firist, ta zo can. 67Da ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau.

Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu, Banazare.”

68Amma ya yi mūsu, ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure.
Waɗansu rubuce rubucen hannu na farko farko suna da ƙofar shiga zakara kuwa ya yi cara


69Da baiwar ta gan shi a can, sai ta sāke gaya wa waɗanda suke tsattsaye a wurin, ta ce, “Wannan mutum yana ɗaya daga cikinsu.” 70Sai ya sāke yin musu.

Bayan ɗan lokaci kaɗan, sai waɗanda suke tsattsaye kusa suka ce wa Bitrus, “Lalle, kana ɗaya daga cikinsu, gama kai mutumin Galili ne.”

71Sai ya fara laʼantar kansa, yana rantsuwa musu, yana cewa, “Ban san wannan mutumin da kuke magana a kai ba.”

72Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu.
Waɗansu rubuce rubucen hannu na farko farko ba su da sau na biyu
Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa, cewa: “Kafin zakara yǎ yi cara sau biyu:
Waɗansu rubuce rubucen hannu na farko farko ba su da sau biyu.
za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka.

Copyright information for HauSRK